Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar Alalam ta bayar da rahoton cewa, a yayin tattaunawar da ta gudana tsakanin Alkazimi da kuma Shamkhani a daren jiya Lahadi a birnin Tehran, bangarorin biyu sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi batun tsaro tsakanin Iran da Iraki.
Shamkhani ya bayyana ayyukan hadin gwiwa na tsaro tsakanin Iran da Iraki na gudana kamar yadda ya kamata, duk kuwa da cewa wannan ba zai hana samun wasu matsalolin da ba a rasa ba.
Ya ce daya daga cikin matsalolin da ya kamata bangarorin su kara mayar da hankali a kansu shi ne batun tsaron iyakokinsu da kuma kara sanya idoa kan duk wani kai komo a kan iyakokin.
Sannan kuma Admiral Ali Shamkhani ya jaddada cewa, ayyukan da wasu ‘yan ta’adda ke gudanarwa a yankin Kurdestan na Iraki da ke iyaka da Iran, na daga cikin abubuwan da suke sanya damu a yankin.
Shi ma a nasa bangaren Firayi ministan kasar ta Iraki Mustafa Alkazimi ya yaba da gagarumin ci gaban da aka samu a dukkanin bangarori tsakanin Iran da Iraki, inda ya jaddada cewa bangarorin biyu za su ci gaba da kara matsa kaimi wajen bunkasa alakarsu da kuma tunkarar duk wani abin da yake a matsayin barazana a gare su, musamman ta fuskar tsaro.
342/